Rahotan Kungiyar ya ce, Najeriya na cikin jeren kasashen da ke Sahun gaba a Nahiyar Afrika, da kungiyoyin ‘yan tawaye ke kafuwa da kuma yadda Akidarsu cikin gajeren lokaci.
A Cewar Rahoton, a watanni 15 na farko shugabanci Muhammadu Buhari, aka samu kungiyoyin tawaye 18 da suka dau makamai.
Rahotan da ke ci gaba da bayyani kan irin tabarbarewar rashin tsaro a Nahiyar Afrika, ya ce a watan Agustan 2016, akalla kasashen Afrika 28 sun fuskanci tashe-tashen hankula, daga ‘yan tawaye da ke dauke da makamai da ‘yan ta’adda 220.
Jamhuriyar Demokradiyar Congo ke kan gaba da yawan kungiyoyin ‘yan tawaye 36, sai Libya da ke Mataki na biyu da yawan kungiyoyi 28.
Afrika ta Kudu ita ce ta Uku da yawan kungiyoyi 26 masu tada kayar baya, yayin da Najeriya ke bi mata a mataki na 4 da kungiyoyi 20 da ke dauke da makamai.
A shekarar 2015, Najeriya ita ce kasa ta 15 mai yawan kungiyoyin ‘yan tawaye, kafin sabon rahotan, CMG, ya kai ta matsayi na 4, akasarin wadanan kungiyoyi sun dau makamai ne domin yaki da gwamnatin shugaba Buhari a cewar Kungiyar.
Rahotan ya kuma Ambato sunan Najeriya a matsayin kasa ta uku da ta fi kashe kudi a fanin tsaro a Afrika, bayan Algeria da Angola. Najeriya na kashe Dala biliyan 4, Algeria na kashe Dala biliyan 10 sai Angola da ke ware Dala biliyan 6 a shekarar.288